
Media Adverts
Media/News Company Ng Ltd
Politics!
BABBAN KWAMITIN UWAR JAM’IYAR APC A GARIN TALATA MAFARA DOMIN KADDAMAR DA FARA RIJISTAR KATIN ZAMA DAN JAMIYAR APC A JIHAR ZAMFARA
Babban kwamitin wanda yazone domin Sa ido da kuma bada Horaswa ga jagororin Jamiyar da ke garin na Talata Mafara,kwamitin yasammu tarbo daga Manyan masu mukaman na jamiyar A garin na talata mafara karkashin jagorancin mai Girma Wakilin talata mafara ta Arewa da mataimakin Sa,A zauren majalisar Jihar Zamfara
Hon•Shamsudeen Hassan Basko da Hon•Aminu Yusuf Ardon Jangebe,Inda suka hadu Domin Tarbo wannan babban kwamiti.
Wakilin Media Adverts ya bayyana cewa Kwamintin sun samu haduwa da sauran Jagororin jamiyar
•Hon Abukakar Musa Mai Naira(Special Adviser Commodity Board)
•Hon Abubakar Muhd Barmo(Permanent Secretary)
•Hon Mustapha Muhammad Kimba
•Hajiya Amina Iliyasu
•Hon Ibrahim Garba(Secretary talata Mafara)
•Hon murtala ishaka Jangebe(DG Government House maintenance)
•Hon Bello Baraden
•Aliyu Aminu
Da sauran masu madafun iko na jamiyar A garin talata mafara.
Kamar yanda Kwamitin ya bayyana cewa,wannan rijistar ana son Ayita babu son rai a ciki yanda dukkanin yayan jamiyar Zasu yi ta cikin aminci da kuma Mutuntawa.
Bisani jagororin sunyi jan kunne ga dukkani wanda keso janyo husuma a cikin wannan sabon shiri na bada Sabon katin zama ainihin dan jamiyar APC a garin na talata Mafara
Dukkanin Masu rike da mukamai na jamiya A garin sunyi amanna da wannan tsari da wannan babban kwamiti yazo dashi kuma zasu bada tasu Gudun muwa domin ganin An samarda Cikkaken Natsuwa da tsari fa wannan sabon tsari.
Media Adverts
Correspondent Zamfara state.