
MEDIA ADVERTS
Media/News Company Nigeria Limited.
KANTOMAN KARAMAR HUKUMAR MULKIN TALATA MAFARA YA DAGE WAJEN GANIN YA TAKAITA MATSALOLIN RASHIN TSARO A YANKIN.
HON•DAHIRU MAI YARA MAFARA(Sole Administrator Talata Mafara)Yagana Da hukumomi daban daban Da suka shafi kare rayukan Alumma da dukiyoyin su.
Kantoma Dahiru Mai Yara da yakasance Jigo kuma Kwararen dan Siyasa mai Burin ganin Talaka cikin walwala da annashuwaa Yacigaba da karbar Kungiyoyi daban daban na fadin garin Talata mafara Domin Tattaunawa dasu Domin Sanin Abunda suke Bukata Domin A taimakesu da kayan aiki Don su cigaba da bada Gudunmuwarsu wajen samarda zaman lafiya mai Dorewa a tsakanin Alummar mu.
Kumgiyoyin da suka hada da:.
•Hukumar Sojoji
•Hukumar Yan sanda
•Kungiyar yan Kasuwa
•Kungiyar Yan Hisba
•Hukumar kulada hanyoyi
•Kungiyar Yan sakai
Da sauran su.
Inda yayi Zama da kungiyoyin Domin Yakara basu dukkanin Goyon baya Domin gudanar da Ayyukan su.
Mai Yara ya bayyana cewa”Karamar Hukumar mulkin Talata Mafara Babu ware a cikin mu Dukkanin mu yan gida daya ne saboda haka Dole mu dage wajen kare hakki da kuma Dukiyoyin alummar mu,yakara dacewa Tabbas Gwamnatin Mai Girma Gwamnan jihar Zamfara,Dr Bello muhammad Matawallen Maradun tayi shiri na gaske Domin Ciyarda jihar Zamfara gaba,hakan yasa Gwamna yayi magana akan bude makaratu Domin Yara maza da mata so sukoma makarantunsu Domin Ilimi Shine Gimshikin Alumma.
Yayi nuni dacewa Alummar Garin Talata Mafara karda suyi kasa a gwiwa Wurin Kai kokarefe korefen su Domin ya isarda dukkanin Korafe korefen su Ga mai Girma Gwamnan jihar Zamfara DR•BELLO MATAWALLEN MARADUN(Shattiman Sokoto).
Inda yakara mika Sakon Godiya Ga daukacin Alumma,Kwansu da kwarkwata bisa irin Goyon baya da yake samu daga alumma matasa,yara harma da tsofafi..
Mai Yara ya jaddada cewa Tabbas Zai yi Iya bakin kokarin sa wajen tabbatar da adalci a tsakanin alummar mu tareda kwatanta gaskiya wurin Ganin Alumma ta kowane bangare sun Amfana da wannan gwamnati Mai Albarka gwamnatin Matawalle.
Saidu Samaila Nakowa
