Baiwa Foundation suna Nan suna cigaba da Gudanar da Shirye shiryen Kayan Abinci da zasu rabawa Alumma a cikin Wannan watan Mai Albarka na Ramadan.

MEDIA ADVERTS
Media/News Company Nigeria Limited

MARAYU DA GAJIYAYU ZASU AMFANA DA TALLAFIN KAYAN ABINCI DAGA BAIWA FOUNDATION KAMAR YANDA SHIRYE SHIRYE KE KAN KAMA

Baiwa Foundation suna Nan suna cigaba da Gudanar da Shirye shiryen Kayan Abinci da zasu rabawa Alumma a cikin Wannan watan Mai Albarka na Ramadan.

Kayan zasu zagaya inda yadace musamman ga Marayu,marassa karfi da gajiyayu,inda Za a Basu kayan Domin Suma suyi Azumi cikin salama kamar dai kowa.

Baiwa Foundation Dake Garin Talata Mafara wacce aka assasa Domin Kawo karshen jahilci da rage Talauci a tsakankanin Alumma,Karkashin Jagorancin Dan Takarar Kujerar Dan Majalisa Mai Wakiltar Talata Mafara da Anka Hon Mika’ilu Barau.