MA’AIKATAR LOCAL GOVERNMENT AND CHIEFTAINCY AFFAIRS ZATA KARA HASKAKA

*Media Adverts*
*Media/News Campany Nigeria Limited.*


*MA’AIKATAR LOCAL GOVERNMENT AND CHIEFTAINCY AFFAIRS ZATA KARA HASKAKA*

*Bayan Amincewar mai Girma Gwamnan jihar zamfara da sauyawa HON•ABUBAKAR MUHAMMAD BARMO(Dan Galadiman Mafara) A matsayin Sakataren din din Daga ofishin Mai Girma Gwamna izuwa Ma’aikatar Kulada alamuran kananan hukumomi da masarautu*

*Hakan ya Sanya Alummar jihar zamfara murna tareda taya Mai Girma Dan Galadiman mafara,murna bisa wannan samun karin matsayi da karramawa daga mai Daraja Gwamnan Jihar Zamfara Wakilin Ma’aikatar yada labarai ta Media Adverts📡(Ibrahim Abdullahi Bernat)ya rahoto cewa lalle Alumma suna cike da farin ciki tareda nuna Annashuwarsu bisa wannan sabon alamari*

*Alummar Jihar Zamfara tabbas suna alfahari salon irin taimakon Dan galadiman mafara a karkashin jagorancin Gwamnatin mai girma Gwamnan jihar zamfara DR BELLO MATAWALLEN MARADUN(Shattiman Sokoto) Saboda yana taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin azikin da samarda cigaba kyauta a yankuna daban daban na jihar Zamfara*

*Wakilin Ma’aikatar yada labaran ta media Adverts📡Ya kara dacewa HON ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA(Sadaukin Mafara)Mai Baiwa Mai Girma Gwamnan jihar zamfara shawara Ya taya Shi murna tareda yimasa fatan Alheri,Yace tabbas jihar zamfara zata kara samun cigaba bisa samun jajirtacce kuma namuji tsayayye mai kokarin kare martabar Alumma*

*Abubakar Muhammad Barmo Alkhairin sa ya zagaya ko ina a fadin jihar zamfara Domin kuwa shi mutun ne mai Nagarta kuma Amintacce hakan ne ya janyo Yaro da babban suna yabamasa saboda irin kokarin sa wajen kare hakkin alumma da taimakon marassa karfi,Dan Galadiman Mafara,Zai zo a jerin mutane na farko masu bada Gudunmuwa da tallafi ga alumma wajen gyaran Ilimi,Samarda jari ga matasa,samarda ingantattun Gine gine A ciki da wajen garin Domin Alumma su samu mazauni,Maluman Addini Tabbas yana basu kulawa da duk wani dan siyasa dake garin Da kuma baiwa alumma muhimmanci wanda hakan babbar nasarace*

*Muna taya Mai Girma Hon Abubakar muhammad Barmo Dan galadiman mafara Samun wannan sauyin wurin Aiki Fatan mu Allah yakara dafamasa Kuma ya Taimaka masa*

*Media Adverts Correspondent Zamfara state……..*

Leave a comment