ZA A KAWO KARSHEN TA ADDANCI A JIHAR ZAMFARA:INJI BABBAN MAI BAIWA GWAMNA SHAWARA

*MEDIA ADVERTS*
*Media/News Company Nigeria Ltd.*

*ZA A KAWO KARSHEN TA ADDANCI A JIHAR ZAMFARA:INJI BABBAN MAI BAIWA GWAMNA SHAWARA*

*HON•ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA (Sadaukin Mafara)Special Adviser Commodity Board Ya ayyana cewa Cikin Sabon tsarin Gwamnan jihar zamfara Ne Na yaki da ta addanci A fadin jihar Zamafara yasa ake sauye sauye dakuma maida Wasu Domin Ayi hadaka Mai karfin gaske Domin kawo karshen yan ta adda a jihar,Alamarin na ta addacin Kullun yana karuwa ne a yankuna kauyukan jihar zamfara.*

*Babban mai Baida shawarar ya bayyana cewa,Tabbas mu na wakilan Alumma da sauran wadanda Gwamna ya aminta da maidasu Wureren aikin su dukka domin Taimakawa jihar, bazamuyi kasa a gwiwa ba Domin ganin mun fitar da rayuwar Alummar mu daga fuskantar baraza da zama cikin dar dar,Zamuyi Fito na fito da yan ta adda kamar yanda mai Daraja Gwamnan jihar Zamfara DR BELLO MATAWALLEN MARADUN(Shattiman Sokoto) yayi masu kashedi akan su aje makaman su ko kuma A yake su*

*SHA’ANIN TSARO A JIHAR ZAMFARA TABBAS ZA A KAWO KARSHEN SA BAYAN DUBA IRIN SHIRIN DA ANKAYI NA YARKAR YAN TA ADDA*

*Mai Girma Gwamna ya nemi Goyon bayan gwamnoni da Goyon bayan Gwamnatin tarayya Domin ganin An fitar da alummar jihar zamfara daga cikin ukubar da yan bindiga suka saka jihar ciki,Kama daga: Samarda Kayan aiki irin su makaman yaki,Bindigu da harsashe da kuma motocin yaki Walki Domin shiga kwararo da kwarkwada inda za a yiwa barayin Dirar mikiya Don Wargazar da duk wata mafaka ta barayin da ke cikin dajukan jihar zamfara*

*Mai Naira ya Nuna dumuwarsa da Rashin kwanciyar hankalinsa bisa irin yanda yan ta addan ke ragargazar alummar karkara,yace Abun ba karamar barazana bace saboda babu wanda zaiji dadi ankashin Alumma,Da wannan yayi kira ga alumma Da su cigaba da Addu’a Allah yakara kawo muna dawamammen zaman lafiya a jihar mu ta zamfara.*

*Mai Naira ya Kara jinjinawa mai Girma Gwamnan jihar Zamfara saboda irin kokarin da yakeyi wurin ganin an magance matsalar tsaro*

*Media Adverts Correspondent Zamfara state.*

Leave a comment