MATAWALLE:YA JAGORANCI GABATAR DA ADDU’AR NEMAN ZAMAN LAFIYA A JIHAR ZAMFARA

MEDIA ADVERTS
Media/News Company Nigeria Limited.

MATAWALLE:YA JAGORANCI GABATAR DA ADDU’AR NEMAN ZAMAN LAFIYA A JIHAR ZAMFARA

Gwamnan jihar zamfara Dr Bello matawallen Maradun(Shattiman Sokoto) tareda Sakataren Gwamnatin jihar SSG Kabiru balarabe (Sardaunan Dan Isa) sun jagoranci gabatar da Addu ar neman zaman lafiya a jihar zamfara a babban masallacin jumu ar dake jihar Kan wuri Gusau.

Inda manyan maluma da suka hada da Sarakunan maluman jihar zamfara da Jami’ an gwamnatin sun Hadu a masallacin Domin gudanar da addua ta musamman Akan neman zaman lafiya a jihar zamfara da kasa Baki Daya,

Mai Daraja Zababen Gwamnan Jihar Zamfara His Excellency Hon. (Dr) Bello Muhammad MoN (Matawallen Maradun Shattiman Sokoto) ya bayyana cewa” Mun bullo da wannan tsari bisa irin nasarori da muke gani jami an tsaro na samu akan yan ta Adda shiyas muka zabi A taro ayi addu a tare da Godewa Allah bisa ni imomin sa Garemu”

Gwamnan Yana tare da sauran Alumma a cikin Wannan masallacin Domin ganin ya bada tasa gudunmawa ta kowane fanni. Ku kasance tare da mu Dan Jin yanda Addu’o’in zasu gudan,Wannan shiri tabbas zai taimaka sosai wajen neman Kariyar ubangiji da kuma taimakon Allah Domin yasamar da sauki ga wannan al amari na rashin tsaro a jihar mu ta zamfara.


Media Adverts Correspondent Zamfara.

Leave a comment