FARIN CIKIN ALUMMAR JIHAR ZAMFARA SHINE BABBAN BURIN GWAMNA BELLO MATAWALLE:INJI MAI NAIRA (S•A)

*MEDIA ADVERTS*
*Media/News Company Nigeria Limited.*

*FARIN CIKIN ALUMMAR JIHAR ZAMFARA SHINE BABBAN BURIN GWAMNA BELLO MATAWALLE:INJI MAI NAIRA (S•A)*

*Bayan Bude Network A babban Birnin jihar Zamfara,Babban Amini kuma na hannun Dama Ga Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara HON•ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA (Sadaukin Mafara)Special Adviser Commodity Board,Ya ce babban burin Gwamna Matawalle shine yaga Alumma suna Farin ciki,Inda Yakara Dacewa a karkashin Jagorancin Gwamnatin Bello matawalle Alamarin ta addacin Kullun yana raguwa bisa irin gagarumar nasarar da Jami’an Tsaro ke Samu akan yan ta adda da suka addabi Alumma,Wanda hakan yabaida Damar a bude network A garin Gasau.*

*Babban mai Baida shawarar ya bayyana cewa,Gwamnan Jihar Zamfara DR BELLO MATAWALLEN MARADUN(Shattiman Sokoto) Ya bada dukkanin kulawa da gudummuwa ga Jami’an tsaro Domin Sukara dagewa wajen ganin An kawo karshen dukkanin wani nau’in ta addanci a ciki da wajen jihar Zamfara,Bazamuyi kasa a gwiwa ba Domin ganin mun fitar da rayuwar Alummar mu daga fuskantar baraza da zama cikin dar dar Hakan yasa muka daukin matakin Fito na fito Da barayi, yan ta adda Hakama mai Daraja Gwamnan jihar Zamfara Gwamna Matawalle ya shedawa Jami’an Tsaro Sucigaba da kashin Barayi karda a bari ko guda ya fita da ransa,Domin sun nuna su Ba zaman Lafiya ne tsarin su ba*

*JAMI’AN TSARO SUNYI NASARAR KAMA BARAYI,DA INFOMOMI DA SAURAN MASU TAIMAKA MASU*

*Dayawa an Samu nasarar kama Barayi da masu taimaka masu,Wanda hakan tabbas babbar nasarace yayinda alummar jihar zamfara zasu kara shedawa cewa Gwamnatin Bello Matawalle tayi shiri tsaf Domin kawo karshen ta addanci Da yardar Allah.*

*Mai Naira Yakara dacewa Rufe Network a jihar Zamfara Tabbas yabada nasara Sosai wajen yakar yan Ta adda,ya yinda suka rasa hanyar isar da sakonin su inda suke fama da matsananciyar Yuwa,Hakan yakara bada gudunmuwa yayinda Sojoji suke ta fattakar su ba dare ba rana,Mai Girma Gwamna ya samu jinjina daga takwarorinsa gwamnoni da Gwamnatin tarayya bisa sabin tsarukan da ya bullo da su Domin ganin An fitar da alummar jihar zamfara daga cikin ukubar da yan bindiga suka saka jihar,Yau gashi Cikin iyawar Allah barayi da kansu suna gudu suna barin jihar Zamfara*

*Mai Naira yakara Shedawa Alummar jihar zamfara cewa tabbas yanzu munyi Gwamna wanda yasan makamar Aiki,Wanda baya Zalunci kuma baya Goyon bayan zalunci yana Nuna dumuwarsa da Rashin kwanciyar hankalinsa bisa irin yanda yan ta addan ke ragargazar alummar karkara,yace Abun ba karamar barazana bace saboda babu wanda zaiji dadi ankashin Alumma,Da wannan yayi kira ga alumma Da su cigaba da Addu’a Allah yakara kawo muna dawamammen zaman lafiya a jihar mu ta zamfara.*

*Media Adverts Correspondent Zamfara state.*

Leave a comment