GWAMNA MATAWALLE ZAI FADI ZABE MAI ZUWA 2023-CEWAR MAGOYA BAYAN GOV.YARI DA SEN. MARAFA

*MEDIA ADVERTS*
*Media/News Company Nigeria Ltd.*

*GWAMNA MATAWALLE ZAI FADI ZABE MAI ZUWA 2023-CEWAR MAGOYA BAYAN GOV.YARI DA SEN. MARAFA*

*Dambarwar Siyasar Jihar Zamfara inda rikicin cikin gida na Jamiyar APC a jihar yaketa kara barkewa a tsakanin Ma goya bayan mai Girma Gwamnan jihar Da Yan bangaren Yari da Marafa*

*BABBAN MAI BAIDA SHAWARA GA GWAMNAN JIHAR ZAMFARA:YA CHACHAKI YARI DA KABIRU MARAFA DA DUKKANIN YARAN SU*

*HON•ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA (Sadaukin Mafara)Special Adviser Commodity Board, Jiya a Babban Birnin jihar Zamfara Gusau ya bayayyana rashin Amincewarsa da Tura Sako mai Karfin gaske Zuwa ga dukkanin wani wanda ke kokarin janyo rikici a cikin jamiyar APC mai farin jini a jihar zamfara.*

*Mai Bada shawarar fara Ya jinjinawa Gwamna matawalle bisa irin kokarin da yake yi domin yaki da Ta addanci a jihar zamfara Da kuma irin gagarumar nasara da aka samu akan Yan ta adda*

*Yace” Idan an tuna zaben 2019 wadannan mutane dai daiku masu tada zaune tsaye Sune suka janyo rashin nasara ga kan su saboda irin hadamarsu da handama da babakere,Allah yayi maganin su Ya baiwa Zababben Gwamnan jihar Zamfara Dr Bello Matawallen Maradun wanda yanzu cikin iyawar Allah,Yana tareda Amincewar Allah,Yana tareda Goyon bayan Shugaban Kasa Gen.Muhammadu Buhari da Uwar jamiyar APC takasa*

*Wakilin Media Adverts📡Ibrahim Abdullahi Bernat Ya rahoto cewa Jiya Babban mai Baida shawarar Mai Naira ya bayyana cewa,Tabbas mai Daraja Gwamnan jihar Zamfara DR BELLO MATAWALLEN MARADUN(Shattiman Sokoto)yazama zakaran gwajin dabi a duk fadin arewacin Najeriya da ma Kudu Matawalle yasha Gaban su Domin duk halin da jihar zamfara take ciki bai hanashi yin Ayyukan raya jiha ba,Yakuma kara mai da Hankalinsa wajen ganin Sojojin Najeriya Sun cigaba da yiwa Barayi Luguden wuta a daji Domin samarda zaman lafiya mai dorewa a kauye da birnin jihar*

*Mai Naira yakara dacewa Gwamnan ya yi iya kokarinsa Domin yaga anyi sulhu a jihar Nan Domin a hadu a taimaki alumma baki daya,Amma su masu burin ganin alumma cikin garari kullun burin su rikici ya cigaba da barkewa yanda talaka bazai amfana ba,hakan bai hana Gwamna matawalle Samarda da aikin yi ga matasan mu kulada lafiya da ilimi haka zalika ya samarda Kayan aiki ga jami’an tsaro irin su makaman yaki,Bindigu da harsashe,nakiya da kuma motocin yaki Walki Domin shiga kwararo da kwarkwada inda za a yiwa barayin Dirar mikiya Don Wargazar da duk wata mafaka tasu da ke cikin dajukan jihar zamfara*

*Daga karshe HON ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA yayi kira na musamman ga dukkanin wani mai madafun iko a cikin wannan gwamnati mai Albarka da su zare damtse domin yaki da duk wani nau’in samarda rikici ko hatsaniya a birni da karkara na wannan jihar tamu sannan yakara jaddada Goyon bayan sa gai mai Girma Gwamnan jihar zamfara DR BELLO MATAWALLEN MARADUN(shattiman Sokoto)*

*Media Adverts 📡Aikin mu ne Samarda ingantatun labaru ga alumma baki daya*.
*Media Adverts Correspondent Zamfara state.*

Leave a comment