
*MEDIA ADVERTS*
*Media/News Company Nigeria Ltd.*
*BARAYI SUNA FICEWA DAGA JIHAR ZAMFARA SAKAMAKON LUGUDEN WUTAN DA SOJOJI KEYI MASU :INJI MAI NAIRA (S•A)*
*HON•ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA (Sadaukin Mafara)Special Adviser Commodity Board,Ya ce Alamarin na ta addacin Kullun jamian tsaro suna samun gagarumar nasara akan yan ta adda da suka addabi Alummar Jihar zamfara musamman Alummar karkara a jihar,To amma cikin iyawar Allah,Karkashin Jagorancin Gwamnatin Matawalle Sojoji sun cigaba da yiwa barayi Luguden wuta har sun fara ficewa da kansu daga jihar.Gwamnatin Mai Girma Gwamna Matawalle ta samu takaitawa da kuma Dakile dukkanin Ta addanci a jihar zamfara*
*Babban mai Baida shawarar ya bayyana cewa,Gwamnan yakara jaddadawa Jami an tsaro cewa tabbas Bazamuyi kasa a gwiwa ba Domin ganin mun fitar da rayuwar Alummar mu daga fuskantar baraza da zama cikin dar dar Hakan yasa muka daukin matakin Fito na fito Da barayi, yan ta adda Hakama mai Daraja Gwamnan jihar Zamfara DR BELLO MATAWALLEN MARADUN(Shattiman Sokoto) ya shedawa Jami an Tsaro Sugiba da kashin Barayi karda a bari ko guda ya fita da ransa,Domin sun nuna su Ba zaman Lafiya ne tsarin su ba*
*SHA’ANIN TSARO A JIHAR ZAMFARA TABBAS YAZO KARSHE*
*Rufe Network a jihar Zamfara Tabbas yabada nasara Sosai wajen yakar yan Ta adda,ya yinda suka rasa hanyar isar da sakonin su inda suke fama da matsananciyar Yuwa,Hakan yakara bada gudunmuwa yayinda Sojoji suke ta fattakar su ba dare ba rana,Mai Girma Gwamna ya samu jinjina daga takwarorinsa gwamnoni da Gwamnatin tarayya bisa sabin tsarukan da ya bullo da su Domin ganin An fitar da alummar jihar zamfara daga cikin ukubar da yan bindiga suka saka jihar,Yau gashi Cikin iyawar Allah barayi da kansu suna gudu suna barin jihar Zamfara*
*Mai Naira yakara Shedawa Alummar jihar zamfara cewa tabbas yanzu munyi Gwamna wanda yasan makamar Aiki,Wanda baya Zalunci kuma baya Goyon bayan zalunci yana Nuna dumuwarsa da Rashin kwanciyar hankalinsa bisa irin yanda yan ta addan ke ragargazar alummar karkara,yace Abun ba karamar barazana bace saboda babu wanda zaiji dadi ankashin Alumma,Da wannan yayi kira ga alumma Da su cigaba da Addu’a Allah yakara kawo muna dawamammen zaman lafiya a jihar mu ta zamfara.*
*Daga Karshe Mai Naira Ya jinjinawa Gwamnan domin yace fasihi ne kuma Hazikin Gwamnan wanda yayi abun ayabamasa*
*Media Adverts Correspondent Zamfara state.*







