GWAMNA MATAWALLE ZAI FADI ZABE MAI ZUWA 2023-CEWAR MAGOYA BAYAN GOV.YARI DA SEN. MARAFA

*MEDIA ADVERTS*
*Media/News Company Nigeria Ltd.*

*GWAMNA MATAWALLE ZAI FADI ZABE MAI ZUWA 2023-CEWAR MAGOYA BAYAN GOV.YARI DA SEN. MARAFA*

*Dambarwar Siyasar Jihar Zamfara inda rikicin cikin gida na Jamiyar APC a jihar yaketa kara barkewa a tsakanin Ma goya bayan mai Girma Gwamnan jihar Da Yan bangaren Yari da Marafa*

*BABBAN MAI BAIDA SHAWARA GA GWAMNAN JIHAR ZAMFARA:YA CHACHAKI YARI DA KABIRU MARAFA DA DUKKANIN YARAN SU*

*HON•ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA (Sadaukin Mafara)Special Adviser Commodity Board, Jiya a Babban Birnin jihar Zamfara Gusau ya bayayyana rashin Amincewarsa da Tura Sako mai Karfin gaske Zuwa ga dukkanin wani wanda ke kokarin janyo rikici a cikin jamiyar APC mai farin jini a jihar zamfara.*

*Mai Bada shawarar fara Ya jinjinawa Gwamna matawalle bisa irin kokarin da yake yi domin yaki da Ta addanci a jihar zamfara Da kuma irin gagarumar nasara da aka samu akan Yan ta adda*

*Yace” Idan an tuna zaben 2019 wadannan mutane dai daiku masu tada zaune tsaye Sune suka janyo rashin nasara ga kan su saboda irin hadamarsu da handama da babakere,Allah yayi maganin su Ya baiwa Zababben Gwamnan jihar Zamfara Dr Bello Matawallen Maradun wanda yanzu cikin iyawar Allah,Yana tareda Amincewar Allah,Yana tareda Goyon bayan Shugaban Kasa Gen.Muhammadu Buhari da Uwar jamiyar APC takasa*

*Wakilin Media Adverts📡Ibrahim Abdullahi Bernat Ya rahoto cewa Jiya Babban mai Baida shawarar Mai Naira ya bayyana cewa,Tabbas mai Daraja Gwamnan jihar Zamfara DR BELLO MATAWALLEN MARADUN(Shattiman Sokoto)yazama zakaran gwajin dabi a duk fadin arewacin Najeriya da ma Kudu Matawalle yasha Gaban su Domin duk halin da jihar zamfara take ciki bai hanashi yin Ayyukan raya jiha ba,Yakuma kara mai da Hankalinsa wajen ganin Sojojin Najeriya Sun cigaba da yiwa Barayi Luguden wuta a daji Domin samarda zaman lafiya mai dorewa a kauye da birnin jihar*

*Mai Naira yakara dacewa Gwamnan ya yi iya kokarinsa Domin yaga anyi sulhu a jihar Nan Domin a hadu a taimaki alumma baki daya,Amma su masu burin ganin alumma cikin garari kullun burin su rikici ya cigaba da barkewa yanda talaka bazai amfana ba,hakan bai hana Gwamna matawalle Samarda da aikin yi ga matasan mu kulada lafiya da ilimi haka zalika ya samarda Kayan aiki ga jami’an tsaro irin su makaman yaki,Bindigu da harsashe,nakiya da kuma motocin yaki Walki Domin shiga kwararo da kwarkwada inda za a yiwa barayin Dirar mikiya Don Wargazar da duk wata mafaka tasu da ke cikin dajukan jihar zamfara*

*Daga karshe HON ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA yayi kira na musamman ga dukkanin wani mai madafun iko a cikin wannan gwamnati mai Albarka da su zare damtse domin yaki da duk wani nau’in samarda rikici ko hatsaniya a birni da karkara na wannan jihar tamu sannan yakara jaddada Goyon bayan sa gai mai Girma Gwamnan jihar zamfara DR BELLO MATAWALLEN MARADUN(shattiman Sokoto)*

*Media Adverts 📡Aikin mu ne Samarda ingantatun labaru ga alumma baki daya*.
*Media Adverts Correspondent Zamfara state.*

DAN MAJALISA DA ZAI KAFA TARIHI A ZABE MAI ZUWA (2023)HON KABIRU YAHAYA CLASSIC KATAPILA SARKIN AIKI

*ALIYU MU’AZU FOUNDATION In Support Of HON KABIRU YAHAYA CLASSIC CONTINUITY PDP 2023*

*DAN MAJALISA DA ZAI KAFA TARIHI A ZABE MAI ZUWA (2023)HON KABIRU YAHAYA CLASSIC KATAPILA SARKIN AIKI*

*Acikin yan majalisu wakilai A abuja Kabiru Classic ya za ma mutun mai dinbin tarihi da Kyakyawar mu’amala a tsakanin sa Da Alummarsa,Hakan ne babbar nasarar Sa a siyasa da yasa Alumma garin talata Mafara da Anka basu gajiya wajen Bashi dukkanin wani Goyon baya.*


*Classic yayi kira ga alummar garin talata mafara da anka da su zama masu godewa Allah bisa ni imomin da yayi masu su tsaya nan inda Allah ya niimta su a jamiyar PDP Allah shi zai kara bashi nasara cikin sauki 2023,Wannan kalami na Dan majalisar tabbas yakara Masa magoya baya sosai a fadin jihar Zamfara da kuma wasu tsaruka da ya bullo dasu na taimakon Alumma ta fanin karatu,kiyon Lafiya Samarda Aikin yi ga matasa da sauran su*

*Tabbas Zamu Kira Hon Kabiru Yahaya Classis Jajirtaccen Dan Siyasa mai Fada da cikawa Saboda alummar talata mafara da anka suna bada sheda akan ka kai mutun ne mai taimako kuma mai kaunar duk wani masoyin Taimakon Alumma*

*Abaka kyauta cikin girmamawa da mutuntawa da murmushi da fara a wannan sai classic hakan yasa bashikada makiya kuma komai nasa yanayi ne domin Allah*

*Hon kabiru yahaya classic lalle wakilcinka nagari kuma nagartacce a garin talata mafara dare darana kana aiki domin samarda da nasara irin yanda ka maida taimakon alumma aikin ka na kullun kullun*

*HON KABIRU YAHAYA CLASSIC muna yimaka Fatan alheri Agareka Allah Ubangiji yakara yimaka muwafaka Allah yakara darajaka kuma yakara daukaka*

*Nagartattun Halayen ka koda yaushe suke kara maka farin jini da soyayyar Al, umma. Burinsa har kullun shine yaga Al,ummarsa cikin Farinciki da nishadi. Allah ya cigaba da baka ikon sauke nauyinda kekanka na wannan Matsayi*

*Tabbas Akwai Kyakkyawar Mu’amala Ga Halaye Masu Dimbin Yawa Abun Koyi Atattate dashi bazakasan Da Hakanba Sai Ka kusantoshi Alokacin zaka Tabbatar da Maganata*

*Babban Mataimaki na Musamman Acikin Siyasar Hon Kabiru Yahaya Classi,Alhaji Aliyu mu’azu muna yimaka fatan allah yakara baku nasara*

*Aliyu mu’azu barka da kokari*

*Saidu Samaila Nakowa*
*Secretary of the Foundation*

GWAMNAN JIHAR ZAMFARA ZAIYI NASARA AKAN DUK WANI MAI KOKARIN KAWO RIKICI CIKIN ALUMMA DAMA JAM’IYA BAKI DAYA:INJI HON •ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA (S•A)

*MEDIA ADVERTS*
*Media/News Company Nigeria Limited*


*GWAMNAN JIHAR ZAMFARA ZAIYI NASARA AKAN DUK WANI MAI KOKARIN KAWO RIKICI CIKIN ALUMMA DAMA JAM’IYA BAKI DAYA:INJI HON •ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA (S•A)*

*A wata ganawa da Babban Mai Baida shawara ga Mai Girma Gwamnan jihar Hon Abubakar Musa mai Naira Mafara ya bayyana cewa tabbas Gwamnan jihar zai Yi nasara akan dukkanin wasu kana nan kwari Masu ganin zasu iya kawo rikici acikin Alumma da ma jihar Zamfara baki daya,Jagoran taimakon Alummar garin talata Mafara HON ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA (Special Adviser) ya bayyana cewa karkashin Jagorancin Gwamnatin Dr Bello Matawallen Maradun(MON)(Shattiman Sokoto) Mai Girma Gwamnan jihar Zamfara zaiyi nasara akan dukkanin wani mai kokarin kawo ta shin hankali ga alumma dama jamiyar APC baki daya.*

*Rakicin jam’iyar da fara tun ranar da akayi taron gaba daya na yan yan Jam’iyar APC a jihar Zamfara ranar 13/11/2021 Da wasu suke ganin anyimasu ba dai dai ba,Sha anin Tsaro a jihar Zamfara ya zamo abu wanda ya addadabi alumma yayinda alumma keta kawo shawarwari daban daban Domin Ganin Gwamnatin tayi maganin ta’addanci a fadin jihar Zamfara farfado Kamfanonin Domin su taimaka Alumma su samu aikinyi da abun dogaro da kansu yanda zasu gujewa duk wani aiki Da zai janyo koma baya ga jihar Da kuma rage Matsalar rashin tsaro domin samarwa matasa ayyukan yi,zai kuma taimakawa Manoman Jihar zamfara Yanda taki,Abinci da sauran su za su samu cikin jiha kuma cikin sauki*

*Hon Abubakar Musa Mai Naira ya tabbatar dacewa lalle Gwamnatin matawalle Gwamnatice mai Fada da cikawa hakan ne zai sa Alumma sufito kwansu da kwarkwata suyi Zabe Domin Ganin Gwamnan yacigaba da inganta rayukan Alumma da ma jihar baki daya alummar karkara zasu amfana da Samun zaman lafiya da natsuwa kuma su koma kan sana ar su ta noma Domin Gwamnati zata bada takin Noma,kamar yanda kamfanin yin taki zai dage sosai wajen samarda da ingantaccen takin noma Domin Jihar tamu Noma ne Abun tinkahon mu.*

*Ma Naira ya jadadda cewa Lalle matawalle yazama jagoran tabbatar da zaman lafiya ga wannan jihar tamu in da yake fadi tashi dare da rana Domin ciyar da jihar nan tamu gaba da wannan tsari zamu cigaba da amfani a wannan gari namu mai albarka domin tantance Jagorori masu manufar samarda cigaba ga wannan gwamnati mai albarka….*

*Special Adviser Mai Naira yakara dacewa Mai girma gwamnan jihar zamfara(DR BELLO MATAWALLEM MARADUN(Shattiman sokoto) Duk wani mai Ganin yana jayayya da Ikon Allah to yasani karshen za kunya a jihar Zamfara,Yabaiwa Naziru Dan fulani fulani matashi kwamishina domin shiman yabada tashi Gudun muwa kara taimakawa wannan gwamnati da kamfanonin jihar wajen samarda ingantatun ayyuka ga alumma baki daya*

*Gwamnatin Matawalle Wannan tsari na samarda zaman lafiya ga alumma tabbas zai taimaka sosai inda komai zai dai daita a samu cigaba musamman samarda in gantatun Kamfanoni ga wannan jiha tamu tabbas zai taimakawa alumma sun amfana da wannan gwamnati.muna Rokon Allah ya mai maita Domin Tabbas gwamnati mai Amfanar da talakawa kuma gwamnatice mai Baiwa matasa Dama*

*Ayi siyasa da Hujja,A taimaki Alumma Domin Shine Zai kawo nasara Colin sauki ga KO wane mai Mukami.*


*SAIDU SAMAILA NAKOWA*
*Media Adverts Correspondent Zamfara state.*