NA MAIDA HANKALINA WAJEN GANIN NA BAIWA MATASA TALLAFIN KARATU INJI DAN MAJALISA MAI WAKILTAR T/MAFARA TA AREWA*

*Media Adverts*
*Media/News Company Ng Ltd.*

*NA MAIDA HANKALINA WAJEN GANIN NA BAIWA MATASA TALLAFIN KARATU INJI DAN MAJALISA MAI WAKILTAR T/MAFARA TA AREWA*

*HON SHAMSUDEEN HASSAN BASKO(Dan Buran Talata Mafara)Dan majalisa mai wakiltar Talata Mafara A zauren Majalisa na Jihar Zamfara Rahoton Da Wakilin Ma’aikatar yada labarai ta Media Adverts*

*Dan Majalisan ya bayyana hakane a yayin tarbo babban kwamitin da Uwar jamiya Ta turo dasu a garin Domin Kaddamar da fa aikin yankar katin Zama ainihin dan jamiyar APC a jihar zamfara,Inda ya ke cewa “Na maida Hankalina wajen Ganin na baiwa matasa tallafin Karatu kyauta ,Tallafin kudin magani da samarda Aikin yi ga matasan yankin na talata Mafara ta arewa*

*Alummar garin Talata Mafara Sun bada shedar wannan tabbas gaskiyane Saboda A halin yanzu mutane da yawa suna nan suna karatu a makarantu daban daban a fadin Najeriya,Sakamakon Tallafin da suka samu daga dan majalisan,Wanda ya ware makudan kudade Domin baiwa wannan shiri na tallafin karatu Kyakyawar kulawa da goyon baya yanda matasa zasu Samu ilimi cikin sauki da Garahusa.*

*A wata Ganawa da Dan Majalisan ya bayyanacewa cewa “Shi matashi ne Domin haka Dole yayi kishin matasa” A fanin baiwa matasa kulawa,garin talata mafara tabbas sunyi dacen wakili ya taimaka sosai wajen rage Tallauci da yan zauna gari banza in da ya samar masu da aikin yi da kuma wayar da kan Alummar yankin Talata mafara ta arewa Domin su san halinda jiha takeci da kuma samarmasu mafita ta yanda zasu dogara da kansu da kuma tabbatar da an samu cigaba a tsakankanin matasan mu,man hajar zata bada dama ga talakawa su isarda korafe korafen su ga gwamnati domin Ayimasu gyar.*

*Ma’aikatar Media Adverts ta yada labarai📡tayi shirin Yada muhimman labarai ga alumma baki daya,Da kuma Wayar da kan Alumma Musamman a wannan lokaci da Alumma suke cikin halin neman agaji da tallafi mussamman daga wurin masu madafun iko.*

*Muna kira Ga jagorori da sukara jajircewa wajen ganin Sun taimaki alumma,matasa,maza da mata Domin hakan ne mafita Wurin ginuwar alumma akan turba ta gari da kuma samun rayuwa mai inganci*

*Media Adverts*
*Correspondent Zamfara state*