MAI GIRMA MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR ZAMFARA:YASHA ALWASHIN TSAYIN DAKA DOMIN KAWO KARSHEN TA’ADDANCI A CIKIN JIHAR ZAMFARA

*Media Adverts*
*Media/News Campany Ng Ltd.*

MAI GIRMA MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR ZAMFARA:YASHA ALWASHIN TSAYIN DAKA DOMIN KAWO KARSHEN TA’ADDANCI A CIKIN JIHAR ZAMFARA

A Jiya ne Ya lashi takobin zasuyi tsaye tsayin daka domin ganin matsalar tsaro ta kau acikin jahar zamfara da ikon Allah a wajen wani taro na Jiga jigan jamiyar Ta PDP reshen jihar zamfara.

Ya kamata mutunatar da kanmu abunafarko mukoma ga Allah madaukakin sarki mubi dokokin Allah sau da qafa mubaiwa dukkanin mai haqqi haqqinsa a matsayin mu na ƴan Nigeria kuma musulmai
Mukasance masu aikata gaskiya Acikin dukkanin lamurranmu cewar muna buƙatar juna domin samun ingantacciyar rayuwa

Ya kamata mu sani cewa lokacin faɗa da juna yawuce ya zama abin ƙyamar, kuma yanzu ne muke buƙatar zama tare domin gina ƙasar mu da jaharmu abar alfahari Aduniya🇳🇬

Kada mu rushe ginin da iyayen wannan kasa suka yi lokacin kafata, abin kunya ne akanmu mubari wani banbanci dake tsakanin mu ya rabamu da juna

Sannan yana daya daga cikin hakkokin dake kanmu Amatsayinmu na shugabanni tubdaga shugaban kasa har zuwan kasa mukasance mun ɗauki matakai da al’umma zasuyi zirga-zirga aminci batare da wata fargaba ba

Anan nake kira ga hukumomi su sauke nauyin dake kansu na kula da rayuka da dukiyoyin al’umma

Allah yakarakare Muda irin Afkuwar mummunan al,amari anan gaba. Allah yajikan waɗanda suka rasu kuma ya zaunar da ƙasar mu lafiya. Ameen ya Rabbi

Saƙo daga: mataimakin Gwamnan zamfara *Barrister Mahadi Aliyu Gusau*

Comrd Abdul Tela
Media Adverts Correspondent Zamfara state.

Leave a comment