TSARO ZAI SAMU INGANTACCE A JIHAR ZAMFARA:INJI BABBAN MAI BAIDA SHAWARA GA GWAMNAN JIHAR ZAMFARA

*Media Adverts*
*Media/News Company Nigeria Ltd.*

*TSARO ZAI SAMU INGANTACCE A JIHAR ZAMFARA:INJI BABBAN MAI BAIDA SHAWARA GA GWAMNAN JIHAR ZAMFARA*

*HON•ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA (Sadaukin Mafara)Special Adviser Commodity Board,Ya ce Alamarin na ta addacin Kullun yana karuwa ne a yankuna kauyukan jihar zamfara,To amma cikin iyawar Allah,Gwamnatin Tarraya tayi shirin Hada karfi da karfe Domin yaki da Ta addanci a jihar zamfara*

*Babban mai Baida shawarar ya bayyana cewa,A matsayin mu na wakilan Alumma tabbas, muma bazamuyi kasa a gwiwa ba Domin ganin mun fitar da rayuwar Alummar mu daga fuskantar baraza da zama cikin dar dar,Zamuyi Fito na fito da yan ta adda kamar yanda mai Daraja Gwamnan jihar Zamfara DR BELLO MATAWALLEN MARADUN(Shattiman Sokoto) yayi masu kashedi akan su aje makaman su ko kuma A yake su*

*SHA’ANIN TSARO A JIHAR ZAMFARA TABBAS ZA A KAWO KARSHEN SA BAYAN DUBA IRIN SHIRIN DA ANKAYI NA YARKAR YAN TA ADDA*

*Mai Girma Gwamna ya nemi Goyon bayan gwamnoni da Goyon bayan Gwamnatin tarayya Domin ganin An fitar da alummar jihar zamfara daga cikin ukubar da yan bindiga suka saka jihar ciki,Kama daga: Samarda Kayan aiki irin su makaman yaki,Bindigu da harsashe da kuma motocin yaki Walki Domin shiga kwararo da kwarkwada inda za a yiwa barayin Dirar mikiya Don Wargazar da duk wata mafaka ta barayin da ke cikin dajukan jihar zamfara*

*Mai Naira ya Nuna dumuwarsa da Rashin kwanciyar hankalinsa bisa irin yanda yan ta addan ke ragargazar alummar karkara,yace Abun ba karamar barazana bace saboda babu wanda zaiji dadi ankashin Alumma,Da wannan yayi kira ga alumma Da su cigaba da Addu’a Allah yakara kawo muna dawamammen zaman lafiya a jihar mu ta zamfara.*

*Media Adverts Correspondent Zamfara state.*

Leave a comment