GWAMNAN JIHAR SOKOTO:YAKAWO ZIYARAR JINJINA WA GWAMNAN JIHAR ZAMFARA BISA SAMUN NASARA AKAN YAN TA ADDA*

*MEDIA ADVERTS*
*Media/News Company*

*GWAMNAN JIHAR SOKOTO:YAKAWO ZIYARAR JINJINA WA GWAMNAN JIHAR ZAMFARA BISA SAMUN NASARA AKAN YAN TA ADDA*

*Gwamnan jihar sokoto RT•HON AMINU WAZIRI,Ya iso jihar zamfara domin nuna farincikinsa da jinjinawa gwamnan jihar Zamfara DR BELLO MATAWALLE MARADUN(Shattiman Sokoto)*

*Gwamnan jihar Sokoto yayinda yake jawabi yace “Muna ta ganin nasarori da jami’an tsaro ke samu akan barayi da yan ta adda a fadin jihar zamfara,hakan ne yasa nazo domin taya gwamnan murna tareda Bashi lambar yabo bisa wannan gagarumar nasara lalle Wannan abun Azo ayabane Jihar Ta samu kwanciyar hankali a cikin kwana 2 Na shinfida wannan dokoki”*

*His Excellency Dr Bello Matawallen Maradun MON(Shattiman Sokoto)Jagoran jamiyar APC a jihar Zamfara*
*Yashedawa Mai Girma Gwamnan jihar Sokoto waziri cewa Matsalar tsaro a jihar ta zama tamkar wuta ce ake ta kara zuba mata man fetur a kwanakin baya Amma yanzu cikin iyawar Allah,Gwamnatin tarraya da hadaka da gwamnatin jihar da sauran masana akan sha’anin tsaro aka duba yiyuwar amfani da wannan sabon shiri gashi ankowa karshen wannan ta addanci a jihata,Dole mu yabama jami’an tsaro masu yaki da wadannan yan ta Adda gashi yanzu jihar ta samu sauki*

*inda Mai Girma Gwamnan jihar Sokoto yake cewa “Ada idan munzo jihar zamfara jajantawa Gwamna matawalle mukeyi bisa karan batta da da barayi keyi a cikin jihar to Amma yanzu gashi cikin iyawar Allah mun shigo jihar Domin tayashi murna Don kawo karshen ta addanci a fadin arewacin najeriya ba ma zamfara kadai ba,Gwmma waziri shima ya dauri damarar amfani da wadan nan tsarukan na gwamnan jihar Zamfara kuma yasha alwashin bada ruduna ta sojoji da kuma Duk wata Gudunmuwa da jami’an tsaro zasu bukata wurin tabbatar da sun samarda tabbataccen zaman lafiya*

*GWAMNA MATAWALLE YACE MUN GODE ALLAH BISA WANNAN GAGARUNAR NASARA*

*Da Wannan muke kira ga Daukacin alummar jihar zamfara da su cigaba da Addu a domin taimakawa Gwamnonin wajen neman mafita ga wannan matsalah ta rashin tsaro a yankin arewacin Najeriya,lalle wannan sabon tsarin Alummar jihar zamfara zasu samu sukuni da zaman lafiya.*

*Daga karshe Gwamnan matawalle yayi mutukar farin cikin wannan ziyara da takwaransa ya kawo masa,kuma yace tabbas wannan alamar nasarar gwamnatin mu ce,Fatan Mu Allah yakara taimakon jami’an tsaro Domin su cigaba da kokari wajen ganin an kawo karshen ta addanci a fadin jihar zamfara*.

*Media Adverts*
*Correspondent Zamfara state*

Leave a comment