
*MEDIA ADVERTS*
*Media/News Company Nigeria Ltd.*
*BABBAN MAI BAIDA SHAWARA GA GWAMNAN JIHAR ZAMFARA:YA JINJINAWA GWAMNA MATAWALLE*
*HON•ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA (Sadaukin Mafara)Special Adviser Commodity Board,Ya jinjinawa Gwamna matawalle bisa irin kokarin da yake yi domin yaki da Ta addanci a jihar zamfara Da kuma irin gagarumar nasara da aka samu akan Yan ta adda*
*Anyake Service,An rufe gidajen manfetur,An Dakatar da amfani da mashuna masu culoci,And Rufe kasuwanni,An Rofe Bodoji na jihar Zamfara Dukka wannan Tsarukane da mai Girma Gwamna ya bullo dasu Domin dakile dukkanin wani shiri yan Ta adda,jami an Tsaro dare darana Luguden wuta suke tayiwa barayi,An kashe dama da barawo 1,000 And Kama Sama da barawo 80,A kalla barawo 3,000 suna cikin mawuyacin hali ga yunwa ga Tashin hankali Fatan Mu Allah yakara bada Nasara akan Barayin a kashe su gaba daya*
*Babban mai Baida shawarar ya bayyana cewa,Tabbas mai Daraja Gwamnan jihar Zamfara DR BELLO MATAWALLEN MARADUN(Shattiman Sokoto)yazama zakaran gwajin dabi,domin gwamnan a wata tattaunawa da manema labarai yace “Munbi barayi ayi sulhu amma tunda sunki Lalle yanzu kam Zamu cigaba da aikasu Lahira chan su amsa tamboyoyi,Gwamnan jihar zamfara Yayi nuni dacewa sojojin najeriya Sunata Luguden wuta ga barayi a cikin daji kuma Ga yunwa rashin manfetur ga baburan su,a haka zasu tabbata Su mutu yanda zaman lafiya Zai inganta.*
*Sha’anin tsaro tabbas yazo karshe bi’izinin Allah Domin gwamnan jihar mutun ne tsayayye yayinda yayi kira ga daukacin Alumma Dasu Taimakawa Doka,wurin gujewa taimakawa barayi da gudunmuwa kowace iri kama daga siyar masu da babura,ko kai masu manfetur Domin gwamnan yasha alwashin tarwatsa barayin tunda Basu san yakamata ba da kimar alumma.*
*Mai Naira yakara dacewa Gwamnan ya Samarda Kayan aiki irin su makaman yaki,Bindigu da harsashe da kuma motocin yaki Walki Domin shiga kwararo da kwarkwada inda za a yiwa barayin Dirar mikiya Don Wargazar da duk wata mafaka ta barayin da ke cikin dajukan jihar zamfara*
*Mai Naira ya Nuna jindadinsa bisa irin yanda jami an tsaro ke ragargazar barayi da su ka addabi alummar karkara,Daga Karshe ya jinjinawa Gwamnan jihar bisa nasarar da jami’an tsaro ke samu akan yan Ta adda yakuma yi addu’a Allah ubangiji yakara kawo zaman lafiya mai Dorewa A jihar Zamfara*
*Media Adverts Correspondent Zamfara state.*