BARAYI SUNA FICEWA DAGA JIHAR ZAMFARA SAKAMAKON LUGUDEN WUTAN DA SOJOJI KEYI MASU :INJI MAI NAIRA (S•A)

*MEDIA ADVERTS*
*Media/News Company Nigeria Ltd.*

*BARAYI SUNA FICEWA DAGA JIHAR ZAMFARA SAKAMAKON LUGUDEN WUTAN DA SOJOJI KEYI MASU :INJI MAI NAIRA (S•A)*

*HON•ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA (Sadaukin Mafara)Special Adviser Commodity Board,Ya ce Alamarin na ta addacin Kullun jamian tsaro suna samun gagarumar nasara akan yan ta adda da suka addabi Alummar Jihar zamfara musamman Alummar karkara a jihar,To amma cikin iyawar Allah,Karkashin Jagorancin Gwamnatin Matawalle Sojoji sun cigaba da yiwa barayi Luguden wuta har sun fara ficewa da kansu daga jihar.Gwamnatin Mai Girma Gwamna Matawalle ta samu takaitawa da kuma Dakile dukkanin Ta addanci a jihar zamfara*

*Babban mai Baida shawarar ya bayyana cewa,Gwamnan yakara jaddadawa Jami an tsaro cewa tabbas Bazamuyi kasa a gwiwa ba Domin ganin mun fitar da rayuwar Alummar mu daga fuskantar baraza da zama cikin dar dar Hakan yasa muka daukin matakin Fito na fito Da barayi, yan ta adda Hakama mai Daraja Gwamnan jihar Zamfara DR BELLO MATAWALLEN MARADUN(Shattiman Sokoto) ya shedawa Jami an Tsaro Sugiba da kashin Barayi karda a bari ko guda ya fita da ransa,Domin sun nuna su Ba zaman Lafiya ne tsarin su ba*

*SHA’ANIN TSARO A JIHAR ZAMFARA TABBAS YAZO KARSHE*

*Rufe Network a jihar Zamfara Tabbas yabada nasara Sosai wajen yakar yan Ta adda,ya yinda suka rasa hanyar isar da sakonin su inda suke fama da matsananciyar Yuwa,Hakan yakara bada gudunmuwa yayinda Sojoji suke ta fattakar su ba dare ba rana,Mai Girma Gwamna ya samu jinjina daga takwarorinsa gwamnoni da Gwamnatin tarayya bisa sabin tsarukan da ya bullo da su Domin ganin An fitar da alummar jihar zamfara daga cikin ukubar da yan bindiga suka saka jihar,Yau gashi Cikin iyawar Allah barayi da kansu suna gudu suna barin jihar Zamfara*

*Mai Naira yakara Shedawa Alummar jihar zamfara cewa tabbas yanzu munyi Gwamna wanda yasan makamar Aiki,Wanda baya Zalunci kuma baya Goyon bayan zalunci yana Nuna dumuwarsa da Rashin kwanciyar hankalinsa bisa irin yanda yan ta addan ke ragargazar alummar karkara,yace Abun ba karamar barazana bace saboda babu wanda zaiji dadi ankashin Alumma,Da wannan yayi kira ga alumma Da su cigaba da Addu’a Allah yakara kawo muna dawamammen zaman lafiya a jihar mu ta zamfara.*

*Daga Karshe Mai Naira Ya jinjinawa Gwamnan domin yace fasihi ne kuma Hazikin Gwamnan wanda yayi abun ayabamasa*

*Media Adverts Correspondent Zamfara state.*

MAI BAIDA SHAWARA YA JINJINAWA GWAMNA MATAWALLE*

*MEDIA ADVERTS*
*Media/News Company Nigeria Ltd.*

*BABBAN MAI BAIDA SHAWARA GA GWAMNAN JIHAR ZAMFARA:YA JINJINAWA GWAMNA MATAWALLE*

*HON•ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA (Sadaukin Mafara)Special Adviser Commodity Board,Ya jinjinawa Gwamna matawalle bisa irin kokarin da yake yi domin yaki da Ta addanci a jihar zamfara Da kuma irin gagarumar nasara da aka samu akan Yan ta adda*

*Anyake Service,An rufe gidajen manfetur,An Dakatar da amfani da mashuna masu culoci,And Rufe kasuwanni,An Rofe Bodoji na jihar Zamfara Dukka wannan Tsarukane da mai Girma Gwamna ya bullo dasu Domin dakile dukkanin wani shiri yan Ta adda,jami an Tsaro dare darana Luguden wuta suke tayiwa barayi,An kashe dama da barawo 1,000 And Kama Sama da barawo 80,A kalla barawo 3,000 suna cikin mawuyacin hali ga yunwa ga Tashin hankali Fatan Mu Allah yakara bada Nasara akan Barayin a kashe su gaba daya*

*Babban mai Baida shawarar ya bayyana cewa,Tabbas mai Daraja Gwamnan jihar Zamfara DR BELLO MATAWALLEN MARADUN(Shattiman Sokoto)yazama zakaran gwajin dabi,domin gwamnan a wata tattaunawa da manema labarai yace “Munbi barayi ayi sulhu amma tunda sunki Lalle yanzu kam Zamu cigaba da aikasu Lahira chan su amsa tamboyoyi,Gwamnan jihar zamfara Yayi nuni dacewa sojojin najeriya Sunata Luguden wuta ga barayi a cikin daji kuma Ga yunwa rashin manfetur ga baburan su,a haka zasu tabbata Su mutu yanda zaman lafiya Zai inganta.*

*Sha’anin tsaro tabbas yazo karshe bi’izinin Allah Domin gwamnan jihar mutun ne tsayayye yayinda yayi kira ga daukacin Alumma Dasu Taimakawa Doka,wurin gujewa taimakawa barayi da gudunmuwa kowace iri kama daga siyar masu da babura,ko kai masu manfetur Domin gwamnan yasha alwashin tarwatsa barayin tunda Basu san yakamata ba da kimar alumma.*


*Mai Naira yakara dacewa Gwamnan ya Samarda Kayan aiki irin su makaman yaki,Bindigu da harsashe da kuma motocin yaki Walki Domin shiga kwararo da kwarkwada inda za a yiwa barayin Dirar mikiya Don Wargazar da duk wata mafaka ta barayin da ke cikin dajukan jihar zamfara*

*Mai Naira ya Nuna jindadinsa bisa irin yanda jami an tsaro ke ragargazar barayi da su ka addabi alummar karkara,Daga Karshe ya jinjinawa Gwamnan jihar bisa nasarar da jami’an tsaro ke samu akan yan Ta adda yakuma yi addu’a Allah ubangiji yakara kawo zaman lafiya mai Dorewa A jihar Zamfara*

*Media Adverts Correspondent Zamfara state.*

BAYA MAI GOYA MARAYU,FITATTCEN DAN SIYASA WANDA YA KWARE WAJEN TAIMAKON ALUMMA

*MEDIA ADVERTS*
*Media/News Campany Nigeria Limited.*

*BAYA MAI GOYA MARAYU,FITATTCEN DAN SIYASA WANDA YA KWARE WAJEN TAIMAKON ALUMMA*

*HON•ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA(Sadaukin Mafara)Special Adviser Commodity Board (S•A) ya zamanto cikin jerin mutanen farko saboda irin mu’amalarsa da mutane karkashin Jagorancin mai Girma Gwamnan jihar Zamfara.*

*A wata Ganawa Da Jagororin Kungiyar Mai Naira foundation Da suka hada da,DR•TIJJANI SULAIMAN,ALHAJI SHAFI’U BUHARI(BIG MAN) DA KUMA MUSTAPHA SABITU (DAN AMERICA) Sunyi Tambihin cewa,Babban mai Baiwa Mai Daraja Gwamnan jihar Zamfara shawara HON ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA(Sadaukin Mafara)Special Adviser Commodity Board*

*Alummar jihar zamfara Sun shedi Mai Naira cewa mutun ne mai kishin jama’a ga fara a ga dunbin halin jibantawa marassa karfi,A cikin tafiyar mai Daraja Gwamnan Jihar Zamfara,Tabbas Mai Naira ya zama sarkin yaki kuma fasihi wajen shiga kauyuka da birane Domin ganin Alumma Sun amfana da gwamnatin matawalle kama daga:Bada tallafin kudade,Gyaran wutar lantarki,Baida magani kyauta,Ginawa mabukata muhallin zama da kuma Samarda aikin yi ga matasa Wakilin Ma’aikatar yada labarai ta Media Adverts📡(Ibrahim Abdullahi Bernat)ya rahoto cewa jagororin kungiyar sun kara dacewa fadin jihar Zamfara ba a tabayin S•A mai farin jini,mai yawan alumma,masoya maza da mata kamar irin mai naira ba,Wanda ba komai ya janyo haka ba sai irin muradin shi na ganin a gina alumma,An taimaki matasa an Tabbatar da gaskiya da adalci a tsakanin jagorari da mabiyansu.*

*Alummar Jihar Zamfara tabbas suna alfahari salon irin taimakon Da Hon.Mai Naira yakeyi a garin na Talata mafara a karkashin jagorancin Gwamnatin mai girma Gwamnan jihar zamfara DR BELLO MATAWALLEN MARADUN(Shattiman Sokoto) Saboda yana taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin azikin da samarda cigaba kyauta a yankuna daban daban na jihar Zamfara*

*Wakilin Ma’aikatar yada labaran ta media Adverts📡Ya kara dacewa HON ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA(Sadaukin Mafara)Mai Baiwa Mai Girma Gwamnan jihar zamfara shawara yayi fice cikin alumma kuma yazama tauraron Duniya inda ko ina Alherinsa akefada*

*Jagora ne mai Nagarta kuma Amintacce hakan ne ya janyo Yaro da babban suna yabamasa saboda irin kokarin sa wajen kare hakkin alumma da taimakon marassa karfi,Sarakuna da Maluman Addini Tabbas yana basu kulawa fiye da duk wani dan siyasa dake garin Domin yana da ladabi da girmama na gaba dashi*

*Daga karshe jagororin Sunyi Addu a tareda Fataj Allah ubangiji yakara kawo zaman lafiya mai Dorewa a fadin jihar mu ta zamfara,kuma yakara taimakawa mai daraja gwamnan jihar Zamfara Wurin samarda cigaba ga wannan jiha ta Zamfara.*

*Media Adverts Correspondent Zamfara state……..*