
*MEDIA ADVERTS*
*Media/News Company Nigeria Ltd.*
*BABBAN MAI BAIDA SHAWARA GA GWAMNAN JIHAR ZAMFARA:YA JAJANTAWA ALUMMAR JIHAR ZAMFARA*
*HON•ABUBAKAR MUSA MAI NAIRA (Sadaukin Mafara)Special Adviser Commodity Board,Ya Jajantawa Alummar jihar zamfara tareda jinjinawa Gwamna matawalle bisa irin kokarin da yake yi domin yaki da Ta addanci a jihar zamfara*
*Babban mai Baida shawarar ya bayyana cewa,Tabbas mai Daraja Gwamnan jihar Zamfara DR BELLO MATAWALLEN MARADUN(Shattiman Sokoto) Domin samarda ingantaccen zaman lafiya a jihar zamfara yabi dukkanin wani tsari Domin ganin jihar ta samu zaman lafiya in gantacce*
*Sha’anin tsaro tabbas yazo karshe bi’izinin Allah Domin gwamnan jihar mutun ne tsayayye kuma mai tausayin alummar sa ne,Mai Girma Gwamna ya nemi Goyon bayan Gwamnatin tarayya,Hukumar sojoji da ta yan sanda da gwamnoni da Goyon bayan maluman addini da kuma Daukacin Alumma Domin ganin An fitar da alummar jihar zamfara daga cikin halin da take ciki*
*Gwamnan ya Samarda Kayan aiki irin su makaman yaki,Bindigu da harsashe da kuma motocin yaki Walki Domin shiga kwararo da kwarkwada inda za a yiwa barayin Dirar mikiya Don Wargazar da duk wata mafaka ta barayin da ke cikin dajukan jihar zamfara*
*Mai Naira ya Nuna dumuwarsa da Rashin kwanciyar hankalinsa bisa irin yanda yan ta addan ke ragargazar alummar karkara,yace Abun ba karamar barazana bace saboda babu wanda zaiji dadi ankashin Alumma,Da wannan yayi kira ga alumma Da su cigaba da Addu’a Allah yakara kawo muna dawamammen zaman lafiya a jihar mu ta zamfara.*
*Daga Karshe ya jinjinawa Gwamnan jihar bisa nasarar da jami’an tsaro ke samu akan yan Ta adda yakuma yi addu’a Allah ubangiji yakara kawo zaman lafiya mai Dorewa A jihar Zamfara*
*Media Adverts Correspondent Zamfara state.*